Mata iyayenmu

Mata 717 Aka Yiwa Fyaɗe Cikin Wata Biyar A Najeriya.

Spread the love

Mata 717 aka yi wa fyaɗe cikin wata biyar a Najeriya, daga watan Janairu zuwa watan Mayun 2020.

Daga:- Aliyu Adamu Tsiga

Babban sufeton ‘yan sandan Najeriya Mohammed Adamu ne ya sanar da hakan ga manema labarai a ranar Litinin bayan ya gana da Shugaba Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Abuja, babban birnin kasar, kamar yadda jaridar Premium Times da kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International suka ruwaito.
Wannan kalamai na Sufeton ‘yan sandan na zuwa ne bayan da a baya-bayan nan aka yi ta samun rahoton matan da aka yi wa fyaɗe a sassan kasar, al’amarin da ya harzuka mutane da dama.

Mohammed Adamu ya ce zuwa yanzu an kama mutum 799 da ake zargi yayin da aka gudanar da bincike kan lamari 631 aka kuma gurfanar da su a kotu, sannan har yanzu ana ci gaba da bincike kan kamarin 52.

Shugaban ‘yan sandan ya ce mai yiwuwa ne matakan takaita zirga-zirgar da aka sanya sakamakon annobar cutar korona ya taimaka wajen samun karuwar fyaɗe a sassan kasar.

“Mun fahimci cewa a yanzu saboda takaita zirga-zirga sakamaon Covid-19, mun samu karuwar yawan masu aikata fyade da cin zarafi. Muna so mutane su fahimci cewa dama can ana aikata wadannan laifuka, amma suna karuwa ne a yanzu.”
Mohammed Adamu ya bayar da tabbacin cewa hukumomin tsaro suna aiki don magance wadanda abubuwa, duk da cewa ba lallai mutane su san irin matakan da ake dauka ba.

Daga karshe shugaban ‘yan sandan ya yi kira ga ‘yan Najeriya su bayar da hadin kai wajen magance matsalar fyade ta hanyar bayar da rahoto da gaggawa ga hukumomi, ”saboda yin shirun yana sa masu aikata laifin na ci gaba da yi.’

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button