
Jami’an hukumar NSCDC a jihar sun kama wadanda ake zargin.
Hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya NSCDC ta tabbatar da cewa wasu mutane biyu sun yi wa wata yarinya ‘yar shekara biyu fyade a karamar hukumar Yauri da ke jihar Kebbi.
Akeem Adeyemi, kakakin hukumar NSCDC a jihar, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce an kawo karar ne ga hukumar daga karamar hukumar.
“An kama mutane biyu da ake zargi da aikata laifin fyade, amma ana ci gaba da gudanar da bincike kuma za a gudanar da shi har zuwa karshensa.
“Abin da zan iya fada kenan a yanzu har sai an kammala bincike,” in ji Mista Adeyemi.
Shima da yake tabbatar da faruwar lamarin, kodinetan hukumar kare hakkin bil’adama ta kasa Hamza Wala, ya ce an kai yarinyar asibiti, inda aka tabbatar da cewa wadanda ake zargin sun yi lalata da ita.
“Akwai rahoton wani likita a yankin, Dakta Bulus Godiya, babban jami’in kula da lafiya na babban asibitin Yauri, wanda ya tabbatar da cewa yarinyar an yi mata fyade ne, kuma yanzu an dauke ta zuwa cibiyar kula da lafiya ta Kalgo domin samun kulawa da magunguna.
“Ba hukumarmu kadai ba, har ma da sauran kungiyoyin kare hakkin mata irin su Yauri Women Development Association, Hisbah Committee, da dai sauransu, duk suna da hannu wajen ganin an gurfanar da wadanda ake zargin bayan an kammala bincike,” inji shi.
Ita ma shugabar kungiyar ci gaban mata ta Yauri (YWDA), Fatima Musa-Bature, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce lamarin ya faru ne a ranar Laraba, 29 ga watan Yuni.
Ta kara da cewa binciken zai yi cikakken bayani akan komai.
Da yake magana kan lamarin, mahaifin yarinyar (an sakaya sunansa) shi ma ya tabbatar da abin da ya faru da ‘yarsa.
“Ya faru da ‘yata, amma ba zan iya magana da yawa akan hakan ba yanzu.”
(NAN)