Mata

Hanan Buhari ta koka kan karancin rahoton fyade a Najeriya

Spread the love

Diyar shugaban kasa, Hanan Buhari, a ranar Juma’a, ta koka kan yadda ake samun karancin rahotannin fyade a kasarnan.

Ms Buhari ta bayyana haka ne a lokacin kaddamar da gidauniyar Hanan Buhari Foundation wanda ya gudana a dakin taro na Banquet na fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Yayin da take gabatar da jawabinta, Ms Buhari ta nanata bukatar magance matsalar fyade tare da jaddada bukatar karya “al’adar shiru”.

Ta ce, “A bisa wani rahoton kididdiga na shekarar 2018 kan mata da maza a Najeriya ta hanyar amfani da bayanan da aka samu daga rundunar ‘yan sanda da ma’aikatar shari’a, ya bayyana cewa yawaitar fyade ga mata da ‘yan mata na karuwa. Tare da karuwar kashi 63 cikin 100 a cikin 2015 zuwa kashi 72.1 a cikin 2016.

“Babu shakka, muna bukatar mu tashi mu karya wannan al’ada ta yin shiru. Musamman yanzu da mata suka fara samun kwarin guiwa wajen bayyana irin yadda ake cin zarafinsu.”

Da take jawabi a sabuwar gidauniyar ta da aka kaddamar, ta ce, “Zan iya cewa gidauniyar za ta yi aiki da wasu manyan hukumomi a kan haka. Za mu mai da hankali kan magance tashin hankali, cin zarafi da fyade.”

Ita ma ma’aikatar harkokin mata, Pauline Tallen ta bayyana haka a wajen kaddamarwar, ta ce, “Kafin in zo ofis, muna da jihohi 12 ne kacal da suka aiwatar da dokar kare hakkin yara, amma da kamfe mai tsauri, ina alfaharin bayyana adadin a yau. ya karu zuwa 34. Jihohi biyu ne kawai suka rage.

“Ina kira ga duk masu kishin kasa da su fara da wannan gwamnati, yayin da muke yaki da cin zarafin mata. Ina yaba wa gidauniyar Hanan Buhari da tawagarku bisa gagarumin aikin da suka yi wajen hada wannan wuri tare da yin kira ga dukkan ‘yan Najeriya masu kishin kasa da su shiga yakar wannan muguwar dabi’a da ke addabar ‘ya’yanmu.”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button