Mata

Kasar Birtaniya za ta tallafa wa ‘yan kasuwa matan Najeriya da dala miliyan 100

Spread the love

‘Yan kasuwa mata a Najeriya za su samu jarin dala miliyan 100 daga Burtaniya, in ji babbar kwamishiniyar Burtaniya a Najeriya, Catriona Laing.

Tallafin ya yi daidai da kokarin tabbatar da daidaito tsakanin jinsi a kasar, da kuma aiwatar da ayyukan ‘Es’ guda uku na Burtaniya, da ke neman ilmantar da ‘yan mata, karfafa mata, da kuma kawo karshen cin zarafin mata da ‘yan mata.

Laing ta bayyana wasu bayanai na jarin a ranar Laraba a taron jinsi da Cibiyar Innovation Center, (PIC), ta shirya a Abuja.

“Birtaniya tana da fannoni uku da ke mai da hankali kan jinsi. ‘Es’ guda uku sun hada da ilmantar da ‘ya’ya mata, karfafawa mata da kuma kawo karshen cin zarafin mata da ‘yan mata,” kamar yadda ta shaida wa mutane a taron.

Kwamishinan ta kuma bayyana cewa, “Birtaniya ta yi aikin ilimi shekaru da dama a yanzu, musamman a arewa maso gabashin Najeriya inda muka tallafa wa karin ‘yan mata miliyan 1.4 da ke zuwa makaranta.

“A bangaren karfafawa, kwanan nan mun kaddamar da wani shiri na dala miliyan 100 ta bankin First Bank of Nigeria wanda zai ba da kudade kai tsaye ga kamfanoni na mata.”

Ita ma da take magana a wurin taron, jakadiyar Amurka a Najeriya, Mary Leonard, ta ce ba da fifiko ga daidaiton jinsi shine muhimmin abu, kuma gwamnatin Amurka tana kashe dala biliyan 200 a duk shekara don rufe gibin jinsi ta hanyar shirye-shiryen jinsi.

Leonard ta ce, “A Najeriya, tawagar Amurka tana aiki don inganta yanayin da ke tallafawa nasarar mata da kuma magance kalubalen da ke mayar da mata baya da kuma karfafawa matan Najeriya damar yin haka.”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button