Rahotanni

Mataimakin Gwamnan Edo Yayi Fita Daga Jam’iyyar APC.

Spread the love

Mataimkin Gwamnan Jahar Edo ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya.

Mataimakin Gwamna Mr Philip Shaibu shine ya bayyana hakan yayin tattauwana da mane ma labarai a yau a Benin, babban birnin Jahar Edo.

Mr philip ya bayyana cewa ya dauki wannan matakin ne domin biye uban gidansa Wato Gwamna Obaseki wanda shine jigo a jam’iyyar APC.

“Ina mai alhinin sanarda ku ficewata daga jam’iyyar APC, wacce jam’iyya ce da muka Gina da jinin jikinmu”

Na Tabbata cewa mun Gina jam’iyyar APC ne domin kawowa Kasarmu ci gaba.

Na fita daga APC cikin bacin rai, sai dai Ina mai sanarda cewa na ficewa domin samawa kaina matsaya.

“Da yardar Allah duk inda Gwamnan Godwin Obaseki yaje, can zanje, kuma da yardar Allah zamuyi nasara”

“Na tabbatar cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari zaiji haushin wannan lamari, sai dai na fice ne domin samawa kaina matsaya”

Haka shima Gwamna Godwin Obaseki ya bayyana ficewarsa daga shugabancin jam’iyyar APC, ya kuma bayyana cewa nan gaba Kadan zai bayyana matsayarsa a siyasance.

Gwamna Godwin ya fice daga jam’iyyar APC ne bayan ziyartar shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadarsa dake Villa.

Daga Abdullahi Muhammad Maiyama

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button