Rahotanni

Mataimakin Shugaban Majalisar Jihar Neja Ya Roki Shugaban Kasa Buhari Kan Ruwan Baro.

Spread the love

A Yau Lahadi ne Mataimakin Shugaban Majalisar Jihar Neja Hon. Jibrin Ndagi Baba, da Wasu Yan Majalisun Tarayya suka Ziyarci Ruwan Baro.

Hon. Ndagi Baba ya yi ziyarar a madadin Mambobin Majalisar Jihar, Senator. Muhammad Bima ya je a madadin Sanatocin Jihar, Hon. Mahmud Agaie yaje a madadin ‘yan majalisun Jihar, Shugaban Karamar Hukumar Chancaga Hon. Abubakar Lalalo ya je a madadin Shuwagabannin Kananan Hukumomin Yankin Zone A.

Ziyarar da Akayiwa Lakabi da BARO PORT MUST BE FUNCTIONAL.

A yayin Ganawa da manema Labarai a Wajen Hon. Jibrin Ndagi Baba, Ya Roki Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Ya Taimaka ayi Aikin tashar Ruwan Baron, Yace Yin Aikin zai Taimaka wajen Habaka Tattalin Arziki, Samawa Matasa Aiki da Farfado da Martabar Jihar da Yankin Arewa dama Kasa Baki Daya.

Hon. Baba yace Barin Aikin Hasarace babba ga Kasa Domin An Zuba Biliyoyin Kudi a lokutan Baya Idan Ba’a Kammala ba To Anyi Hasarar Kudin da Aka Kashe A Baya.

Aikin Ruwan Baron dai Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi Ikirarin Kammala Aikin A lokacin Yakin Neman Zabensa na Shekarar 2019, Sai dai Har Zuwa Yanzu Babu wani Abu da Aka Fara na Aikin, Aikin Dai Yananan Yadda Aka Barshi Tun Bayan Rasuwar Tsohon Shugaban Kasa Umaru Musa Yar Adua.

Ahmed T. Adam Bagas

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button