Kimiya Da Fasaha
Matakan Tsaron Computer Kashi Na Biyu
Wasu shawarwari akan tsaron na’ura (2)
Ana yi wa mutane kutse ta hanyoyi da dama, ya dai danganta ga abunda akeson yi wa kutsen ne. Ga wasu shwarwari da ya kamata mu bi don kare kawunanmu daga fadawa tarkonsu:
- Ka koyi rike sirri
Ka ajiye sirrukanka wadanda za’a iya yi maka kutse da su (sensitive information) a sirrance. Sensitive information sune kamar credit card numbers, passwords, date of birth, security questions/answers, OTPs da sauransu. Wani lokacin sai kaga mutum ya sayar da na’urarsa kuma akwai wadannan sensitive information din a ciki, ko kuwa yana bawa wasu su kai tsaye, ko barinsu wasu suna gani a fili. A zahirin gaskiya wannan kuskure ne. - Kada ka ajiye sirrukanka kara zube
Abun nufi anan shine kada ka ajiye sensitive information a na’urarka kara zube ba tare da ka sanya wasu dabarun boyewa ba kamar encryption, sanya password wajen bude su da sauransu. A shawarce ka nemi takarda ka rubuta copy na su zai fi akan ajiye su a cikin na’urarka. - Kada ka kasance mai yin amfani da lambobin sirri masu sauki
Wannan kuma shine ruwan dare. Misali: 12345, 0000, ranar haihuwa, sunanka, sunan yarinyarka dss wadannan sune misalan lambobin sirri masu saukin canka wanda mafi yawan wadanda suke amfani da su mata ne. Ka kasance mai sanya lambobin sirri masu tsauri hade da symbols, capital/small letters, numbers dss. - Kada ka kasance mai saurin sanya duk wata manhaja a cikin na’urarka
Akwai manhajoji masu hatsari wadanda suke yawo a yanar gizo, wanda kuma yawanci mutane suke fadawa tarkonsu ta hanyar sauke su a cikin na’urorinsu. Kayi hankali da wannan, hakan yana jawowa manyan kamfanoni ma barazana mai tsauri, kuma yayi sanadiyyar sanya mutane da dama cikin hatsari. - Ka rinka kulle wi-fi, bluetooth, location din na’urarka idan baka amfani da su
Akan iya shiga na’urarka ta wadannan hanyoyi ko da baka sani ba. Ka rinka kulle su (turn off) idan baka amfani da su domin gujewa fadawa tarko. - Kayi hankali yayinda ka shiga yanar gizo
Ba kowane link zaka rinka latsawa yayinda kake browsing a yanar gizo ba. Wani lokaci akan iya tura maka link ta facebook, email, whatsapp ko kuma ka gani a wani website ana cewa ka danna ka shiga, idan kuma lamarin yazo da tsautsayi sai a samu matsala. Kayi hankali sosai da irin wadannan domin suna da matukar hatsari, yanar gizo duniya ce wacce ta tara mugaye da muminai wadanda bazaka iya banbance su ba.
Idan har muka bi wadannan shawarwarin da wasu ma, Insha Allahu zamu iya rage saukin yi mana kutse da akeyi da kuma damfara wanda ta zama ruwan dare a yanzu.
Allah ya kare mu, ameen.
Mohiddeen Ahmad
8th June, 2020