Matar Sani danja mansura isa ta fashe da kuka…
Mansura isah matar sani danja tayi kuka da idonta kan sharrin da akayi mata.
Hankalin ta ya matukar tashi a Lokacin da ta samu labarin wani kagaggen Labari kanta daya karade kafofun sada zuminta na zamani cewa tsohowar jaruma mansura isa ta rasu a bisa hadarin mota lamarin da yaja hankalin jarumar tare da yan uwanta zuwa ga Labarin sai dai hakan yasa tayi Bidiyon tana me karyata Labarin ta kuma yi gargadi zuwa ga gidan television na liberTV dasu tabbatar sun karyata Kansu da kansu kan wagga Labari domin jarumar tace tana da Hujja tabbatacciya cewa sune suka fara wallafa labarin mutuwar tata kuma tace idan basu karyata kansu ba lallai zata dauki matakin bin hakkinta kan wagga al’amari…
Tsohuwar jarumar ta fashe da kuka alokacin da take bayani tare da nuna jin haushin ta yadda aka tashi hankalin ‘yan uwanta da masoyanta wannan dai bashi karon farko ba da ake kirkirar labarin mutuwar wani wanda ya samu daukaka acikin harkan film din hausa…