Rahotanni
Matasa a Jihar Oyo, Sun Kone Babbar mota da Lodin Shanu.
Wasu fusatratun Matasa a Garin Saki dake Ibadan Sun Kone babbar mota da ke dauke da lodin shanu.
Wannan al’amari ya farune a lokacin da Motar ta buge wani matashi Ayuba Raji, wanda tayi sanadiyyar Mutuwarsa.
Hatsarin ya farune dalilin gyaran hanyar da ake kanyi yanzu haka, Sai dai mazauna garin na Saki sun zargi drebobin manyan Motar da Tukin ganganci duk da ana Aiki a hanyar.
Mamacin yana Kan mashin ne Babbar motar da ke dauke da Shanu ta Bugeshi ya Mutu, matasan Garin Suka Kone Motar da Shanun Kurmus.
Wannan al’amari ya farune Jiya litinin da karfe 10 na dare a dai dai Mahadar Challenge dake garin Saki a Oyo.
Ahmed T. Adam Bagas