Kungiyoyi

Matasa Masu Zanga Zangar a Rushe Rundunar SARS Sun Kirkiri Jam’iyya.

Spread the love

Yayin da ake ci gaba da zanga-zangar #EndSars a Najeriya matasa sun bijiro da wata jam’iyya da suke yada wa a shafin twitter da sunan sabon jam’iyyar matasa ta ƙkasa.

Tun wayewar garin yau Laraba tambarin jam’iyyar ke yawo a shafin twitter kuma matasa ke neman goyon-bayan juna wajen kafuwarta.

Wasu daga cikin sakonnin da matasa ke wallafa shi ne gangamin su ya wuce na soke SARS domin za su kafa jam’iyyar da za ta kai su ga gacci a Najeriya.

Sai dai Yankin Kudanci Kasar ne kawai ke Yin zanga zangar ta EndSars.

Kuma wannan matakin na zuwa ne saura kwana daya Gamayya Kungiyoyin Arewa ta Fara Zanga Zanga kan Kisan kare dangi da ‘Yan Ta’adda masu garkuwa da mutane da ‘Yan Boko Haram Ke yi a Yankin Arewacin Kasar.

Ahmed T. Adam Bagas

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button