Lafiya

Matasa Ne Ke Yada Covi-19~NCDC.

Kamar yadda mutane da yawa ke kamuwa da cutar a duniya, a bayyane yake a fili cewa cutar tana yaduwa ne tsakanin samari, ba yara ba, wato mutanen da ke tsakanin shekara 20 zuwa 40, kamar yadda muka sani suna matukar yada wannan kwayar cutar, amma waɗanda ke ɗaukar cutar su wahala mutane ne masu shekaru 50 ko sama da haka.

Kashi uku cikin mutane biyar da suka mutu daga CVID-19 shekaru 50 ne da sama da haka; saboda haka dole ne muyi aiki tukuru dukkan mu baki daya, don kare tsofaffi.

Muna gab da bude filin jirgin samanmu, mun saki jiki da tafiya mai nisa, inji Ihekweazu.

Ihekweazu ya nemi mutane da kada su tafi ziyarar jama’a, wanda hakan na iya kara yaduwar cutar.

Hukumar NCDC ta ce ta wallafa sabbin ka’idoji da ba da shawara ga masu rauni, kuma ta bukaci ‘yan Najeriya da su karanta ta.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button