Labarai
Matasan Nageriya sun nemi gafarar Ministan jinkai Sadiya Farouq
A Shafukansu Matasan yan Nageriya ma’abota Kafafen sada zumuntar Zamani suna ta rubutu Mai dauke da sakon neman afwa ga Ministan jinkai da bayarda Agajin gaggawa ga bil’adama Hajiya Sadiya Umar Farouq Kan bisa Zargin ta da sukayi a baya Kan yawan Zabga Karya a Lokacin baya Kan Batun Agajin Tallafin CoronaVirus Hakan ya biyo baya ne sakamakon tarwatsa wuraren boye abincin tallafin Corona a jihohin da dama da matasa sukayi a kwanakin Nan..
A kwanakin baya dai Jama’ar Nageriya da yawa na Kallon Ministan amatsayin makaryaciya Cikin maganganunta Wanda Hakan yasa har Suka saka Mata suna Zubaida ma’ana Mai yawan Karya yanzu dai dama sunce sun gane Gaskiya ba laifinta bane laifin na gwamnoni ne da Suka boye abincin bayan ta mikashi gare su…