Labarai

Matashi ya kashe Abokinsa Akan naira 500 A jahar Kano

Spread the love

A ranar Alhamis din da ta gabata ne rundunar ‘yan sanda reshen jihar Kano ta tabbatar da cewa wani matashi mai suna Haruna Ya’u (c dan shekara 22) Anyi zargin cewa ya kashe abokin nasa, Ibrahim Ibrahim ne sakamakon rikici tsakanin su dashi Akan N500.

Haruna Ya’u,wanda aka fi sani da Dan-Haru mazaunin karamar hukumar Tarauni ne a cikin Kano.

A wata tattaunawa da Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda reshen jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce batun da ake zargi ya kashe Ibrahim Ibrahim kan kudi N500 wanda ba nasa ya caka Masa wuka a kirji, Nan take
marigayin ya mutu

DSP Kiyawa ya ce, “wanda ake zargi da aikata laifin ya amince da aikata laifin”.

Ahmad ‘daya daga cikin wanda ya shaida abin da ya faru, ya ba da rahoton cewa ‘yan mintoci kaɗan kafin abin da ya faru matasan biyu sun tsaya kusa da shi suna fada inda shawarce su da su daina fadan kuma su zauna lafiya.

Kodayake, Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano Habu Sani ya riga ya tabbatar da kamo wanda ake zargin, kuma ana kan gudanar da bincike tare da mayar da batun zuwa sashen binciken’ yan sanda na jihar kano Daga Abdulrashid Abdullahi, Kano

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button