Matashin Da Ya Kera Software Yayi Kudi
Nick D’Aloisio wani matashi ne dan London wanda ya kirkiri wani application mai suna Trimit (Trim it) a shekarar 2011 lokacin yana dan shekara 17.
Aikin Application din shine summarizing din dogon rubutu ya mayar dashi kadan kuma mai ma’ana. Application din ya samu recognition daga kamfanin Apple na US da manyan shahararrun mutane a duniya ciki har da Li ka-Shing wanda ya bawa D’Alosio $300,000 domin yin jarin daukaka application dinsa.
Daga bisani a karshen shekarar 2011 din D’Aloisio ya kara re-designing din app dinsa tare da sanya wasu tsare-tsare sa’annan ya chanja masa suna ya koma Summly. Bayan shekaru biyu a shekarar 2013 D’Aloisio ya sayarwa kamfanin Yahoo app dinsa akan farashi $30 million.
Ka duba fa, a cikin shekaru biyu kacal da fara managing app din ya samu wadannan makudan kudade. Abunda zamu duba anan bayan basirarsa da yayi amfani da ita wajen kirkirar wanann app din da ya samu karbuwa a duniya, manyansu yan kasuwa suna taimaka musu ne da jari domin cigaba, amma mu anan Nigeria ba’a yi, hasali ma sai dai ayi kokarin rufe maka kasuwanci ta hanyar fuskantar matsin lamba. Kuma haka duk wani startup da ka sani ya ginu a duniya sai da sa taimakon wasu. Amma mu hakan din ma yana kara nusar da mu cewa dole mu tashi mu gina na kanmu da kanmu.
Idan kazo Nigeria nan akwai entrepreneurs da suka jima suna harkar nan amma abun mamaki babu yan Arewa cikinsu. Ka duba Seun Osewa (mai Nairaland Forum, founded 2005), Linda Ikeji (started in 2006), Sim Shagaya (Konga, 2012), Opeyemi Awoyemi (WhoGoHost, 2006), ga tarin bloggers da sauransu. Idan kuma kana webmastering ka duba hosting companies duk da ka sani na Nigeria ka binciko na Arewa… abun ba’a cewa komai gaskiya. Wannan dalilin yasa ko lokacin da Zuckerberg yazo Nigeria mukayi ta cece-kucen meyasa bai zo Arewa ba ya tsaya a kudu, ai ko Kaduna ya kamata yazo tunda itace muke ganin centre na technology a Arewa kamar yadda Lagos take a kudu.
Abdul Sadiq ba wai gina startup din bane yake yiwa yau Arewa wahala, a’a samun unique idea da zata ankarar da al’umma ne aiki. Abun ya danganta ne da wane kalar idea mutum yake da. Steve Jobs da kansa yake cewa wata dama da ya samu na modernizing din writing style system zuwa computer-based yasa ya samu nasarar kirkiro kamfanin Apple, yau gashi ya zama mashahuri a duniya. Haka nan Jack Ma yace kayi amfani da koke-koken da mutane sukeyi wajen samun taka damar.
Lokacin da akayi yayin Ponzi Scheme a 2017 ina daga cikin wadanda suka rubuta scripts nata. Na kirkiri Proteena NG tun daga V1.0 har zuwa V3.5 wanda duka yan kudu ne suke saya kuma da su nake harkokin freelancing dina a lokacin. Na karanci yadda suke kutsawa cikin kasuwa su samu karbuwa a startups nasu ta hanyar defeating din duk wani obstacles da zasu samu da kuma uwa uba kashe kudi. Suna zuba kudi su samu kudi sosai. Yanzu ka duba wannan guy din mana Paul Samson. Sai bayan kwana biyu ka ji shi shiru sai kuma kaga ya fito da wata hanyar samun kudi. Bai damu ya kashe millions ba ko da zaiyi asarar su, amma mu ko 10k mutum ya kashe bai samu biyan bukata ba yanzu zakaga mun fara ja da baya. Kasuwanci sai da kudi.
Allah ya taimaka, ameen.
Mohiddeen Ahmad