Kimiya Da Fasaha

Matashiya ‘yar jihar Kano ta kirkiro App na android domin bada rahoton lamarin fyade.

Spread the love

Wata budurwa ‘yar asalin garin Kano, Sa’adat Aliyu ta kirkiro wani manhaja ta android mai suna ‘Helpio App’ domin gabatar da rahotannin lalata da mata.

An fara amfani da ‘Helpio App’ a ranar 6 ga Agusta, 2020, a Playstore.

Ms Aliyu wacce ita ce ta kirkiro Shamrock Innovations, Women and Youth-Centric Tech Innovation Hub a Kano, ta ce kowane mutum na iya ziyartar Playstore a wayar android kuma ya sanya manhajar.

“Kuna iya zuwa Play store, ku neme shi ku girkes shi. Bayan Shigarwa, za ka iya yin rajista ta amfani da imel da kalmar sirri ko dai da Hausa ko Turanci, ”kamar yadda ta fada wa gidan Talabijin na Channels ranar Litinin.

“Ya zuwa yanzu shirin bada tallafi ga wadanda aka ci zarafinsu ta hanyar lalata, Marayu da masu karamin karfi (ISSOL) da Equity Destitute, Child right and Welfare initiative (EDCRAWI) sun rattaba hannu a dandalin.”

Ta fara koyon ilimin IT ne daga dan uwanta a lokacin da take karamar sakandare kuma daga baya ta zama mai koyar da kanta.

Matashiyar ta ce za a fara aikinta na gaba nan ba da jimawa ba kuma an tsara ta ne da fasaha don ci gaba da yin tasiri ga rayuwar mata da mutane ta hanyar ba da shawarwari da samar da mafita.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button