Matsalar Fyade:- Ya yiwa `Yar Shekaru 8 Fyade kotu ta Daureshi shekaru 30 a Neja
Wata kotun majistare da ke Minna, jihar Neja, ta yanke wa wani Tsoho Mohammed Sani Umar, daurin shekara 30 a gidan yari saboda yi wa wata yarinya ‘yar shekara takwas fyade a Karamar Hukumar Chanchaga ta jahar Neja.
Umar ya amsa yayi ma yarinyar fyaden sau biyu kafin ya ba ta N80 don kada ta faɗa wa kowa labarin abin da ya faru.
Da yake yanke hukunci a kan karar, Alkalin Kotun, Safuratu Abdulkareem na Kotun Majistare ta III, dake Minna, ta samu Umar da laifin aikata Fyaden kana ta yanke masa Hukuncin.
Alkalin kotun ya yanke masa hukuncin shekaru 30 a kurkuku, ya kara da cewa hukuncin gidan yari ya yi daidai da Sashe na 18, Sashi na 2 na Dokar Hakkin Yara na shekara ta 2010 na Jahar Neja.
Wani mai fafutukar kare hakkin Dan Adam a jahar Neja, Abubakar Saidu Arah, ya yaba wa kotun kan saurin yanke hukunci a kan me Laifin.
Ya bukaci gwamnati da ta karfafawa hukumar kare hakkin dan adam ta kasa da hukumar kare hakkin yara ta jihar Neja, tare da jaddada cewa ya kamata gwamnatin jihar ta dauki matakai na tabbatar da aiwatar da abin da ya dace kan masu cin zarafin Yara a jahar.
Ahmed T. Adam Bagas