Rahotanni

Matsalar Hanyan Mota;- Sarkin Bida A Jihar Neja, Ya Gana Da Fashola.

Spread the love

Mai Martaba Sarkin Bida kuma shugaban majalisar Sarakunan Jihar Neja. Alhaji. Dr. Yahaya Abubakar Etsu Nupe, ya Kai ziyarar Girmamawa da Bukatar Gyara Hanyar Bida zuwa Minna, ga Ministan Ayyuka Na Kasa, Hon. Babatunde Raji Fashola a Abuja.

Basaraken ya samu Rakiyar Manyan Mutane ‘Yan Kabilar Nupe.

Hanyar Bida zuwa minna dai Ta lalace matuka, ta zama barazana ga Rayuwa da lafiyar Matafiya, Lalacewa Hanyar ta Sanya Kudin Mota yayi tashin Gwauron Zabi, Abaya banyan nan Ana biyan kudin mota Minna zuwa Bida naira 500 ne amma yanzu naira 1500 ne a dalilin Lalacewa Hanyar.

Hanyar Itace Gwamnati Jihar Ta Haramtawa Manya Motoci binta a watan da ya gabata domin a gyara hanyar Inji Gwamnatin Jihar.

Ko Sarkin Kano Aminu Ado Bayero da yaziyarci Takwansa na Bida, Ya Roki Gwamnatin Tarayya da Ta Jiha da su Taimaka su gyara Hanyoyin Jihar.

Idan Baku manta ba Gwamnatin Jihar Tayi Ikirarin ta Bada Gyaran Hanyar ga Kamfanin Gyaran Hanya na DANTATA & SWOE a Watan Febrarun wannan Shekarar, Inda tace za’a gyara Hanyar Cikin Watanni 18, kan Kudi sama da biliyan 2b.

Sai dai Har yanzu Shuru Kakeji Malam. Yaci Shirwa.

Ahmed T. Adam Bagas

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button