Labarai

Matsalar rashin tsaro yazo karshe a Nageriya ~Cewar Bola Tinubu.

Spread the love

Shugaba Bola Tinubu ya ce kasancewar gwamnatinsa mai rikon amana tana sane da matsalar tsaro a Najeriya kuma a shirye take ta magance duk matsalolin da ‘yan Najeriya ke da shi kan lamarin.

Tinubu, wanda mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya wakilta, ya bayyana haka ne a yayin bikin rufe ranar sojojin Najeriya na shekarar 2023 (NADCEL) da kuma cika shekaru 160 na sojojin Najeriya a ranar Alhamis a Ibadan.

Ya tabbatar wa ‘yan Najeriya kudirin gwamnatinsa na magance duk wata barazana da kuma kula da kalubalen tsaron kasa da ke fuskantar kasar cikin kankanin lokaci.

Shugaban ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da yin duk abin da za ta iya kuma kamar yadda kundin tsarin mulki ya ba shi damar tabbatar da tsaron lafiyar ‘yan kasa masu bin doka da oda da hadin kan kasa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button