Matsalar tsaro a Jihar kaduna Sanata Uba Sani Ya Halarci taron masu ruwa da tsaki domin magance Matsalar.
Sanatan ya sanar da Cewa A safiyar yau, na shiga cikin Jerin wata Babbar tattaunawa a jihar Kaduna kan halin rashin tsaro a jihar da kuma matakan gaggawa da suka zama dole a ɗauka domin hana ci gaba da kawo nakasu ga fannin tsaro.
Sanatan Yace Taron wanda Mataimakiyar Gwamnan Jihar Kaduna, Mai girma Dokta Hadiza Balarabe ta jagoranta Taron ya kuma samu halartar takwarana babban abokina, Sanata Abdu Kwari, da Kuma mambobin Majalisar Wakilai, ’yan Majalisar Dokokin Jihar, Kwamishinonin Tsaro na Cikin Gida dana Shari’a, da kuma Shugabannin Kananan Hukumomi.
Mahalarta Taron sun bayarda Gudummawa masu fa’ida da gaskiya tare nemo Hanya wacce zata kunshi masu ruwa da tsaki da kuma baiwa yan jihar Kaduna kwarin gwiwa Wanda mu Masu ruwa da tsaki mun tabbatar da cewa hukumomin tsaro za su samu cikakken goyon baya kan wannan yaki ga ‘yan fashi da masu satar mutane da sauran masu aikata ta’addanci da ke firgita mutanen jihar Kaduna. Hakanan za a tattara mutane gaba daya don daukar matakan da suka dace a tsakanin al’ummominsu don taimakawa jami’an tsaro.
Wannan taron na Kaduna wata manuniya ce a fili cewa masu ruwa da tsaki sun isar da barazanar ga yan fashi da masu satar mutane. Ana buƙatar cikakken goyon baya ga mutanenmu don samun nasara kan sabon ƙudurin.
Sanata Uba Sani gundumar kaduna ta tsakiya.