Matsalar Tsaro A Katsina:- Gwamnatin Tarayya Ta Tura Sojoji Katsina.
Daga Ahmed T. Adam Bagas
Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta tura dakarun Soji Jahar Katsina a Kokarinta Na Kawo karshen Ta’addanci a Yankin.
Jahar ta katsina dai Na fama da tashe tashen hankula Na masu garkuwa da mutane Wanda wannan yayi sanadiyar Salwantar rayuka da dama yasa dubban Mutane Barin Muhallinsu.
Al’ummar Katsina dai sun Dade suna kiraye kiraye ga Gwamnatin Jaha da ta Tarayya Sai dai Gwamnan Jahar Hon. Aminu Bello Masari yace suna Iyaka kokarinsu don Inganta Tsaro a Jahar Sai dai yace Wannan Alhaki Na Soji ya Rataya ne Kan Gwamnatin Tarayya Wajen Tura Sojoji Jahar.
Kawo Yanzu dai Akalla Kananan hukumomi 12 Ne Ke Fama da Matsalar Tsaro a Jahar Cikin 34 da Jahar Take da su Inji Dan Majalisar Jiha mai wakiltar Jibiya a zauren Majalisar Jahar Katsina.