Labarai
Matsalar tsaro a mulkin Buhari Malamai zasu Fara alkunut.
Wani babban Malamin Addinin Musulunci daga bangaren ƙungiyar Izalah Farfesa Mansur Sokoto ya ce lokaci yayi da ya kamata a fara yin ƙunuti akan yadda matsalar tsaro da ya addibi ƙasar nan mussaman yankin Arewa.
Malamin ya tabbatar da haka ne a shafinsa na Facebook a cikin daren Asabar.
Ya wallafa cewa, “masu cewa me ya sa Malamai ba su yi kira ga yin kunuti ba? Sun fadi gaskiya. Lallai lokaci ya yi da ya kamata ayi kunuti akan matsalar tsaro a Najeriya.”.
“Muna fatar a samu ƙira daga shugabanni musamman mai Alfarma Sarkin Musulmi da manyan kungiyoyin addini da fitattun malamai wadanda al’umma take sauraron su”.
Daga ƙarshe ya ce tuni suka fara tattaunawa da junansu malamai domin ganin yadda zai kasance. Rahotan hausa Daily times.