Tsaro

Matsalar Tsaro A Najeriya:-‘Yan Bindiga Sun Kori Mutum Dubu 23 Daga Gidajensu, Inji Hukumar Kula Da ‘Yan Gudun Hijira Ta Majalisar Dinkin Duniya.

Spread the love

Ahmed T. Adam Bagas

Hukumar ta ce kusan mutane dubu 23 ne tashe-tashen hakulla
suka tilastawa barin garuruwansu a shiyyar arewa-maso yammacin Najeriya zuwa cikin Nijar tun daga watan jiya na
Aprilun wannan Shekarar.

Ta ce galibin mutanen sun kaura ne daga jihohin Sakkwato da Zamfara da kuma Katsina.

Wannan bayanin dai na zuwa ne yayin bayanai daga jihar
Katsina ke cewa ‘yan bindinga sun kai hare-hare a kauyuka masu yawa a jihar cikin kwanakin nan.

Idan Ba’a mantaba A Jahar Neja Mah dai ‘Yan Bindigan suna cin karensu Ba Babbaka a Wasu Yan Kunan Jahar musamman Yankin Kananan Hukumomin Shiroro, Rafi, Kagara da Sauransu da ke Nejan.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button