Tsaro
Matsalar Tsaro:- An Kashe mutane 133 Cikin Awanni 24 a Borno da Katsina.

A Yau Laraba ne Aka gudanar da Jana’izar Mutane 52 da yan Bindiga suka Kashe a daren Jiya a Garin Kadisau dake karamar hukumar Faskari ta Jahar Katsina.
Har Ila yau aka yi Jana’izar Mutane 81 da yan Boko Haram suka kashe a garin Poduma dake karamar hukumar Gubio ta Jahar Borno. Jaridar Daily Trust ta Tabbatar da Kisan na Jahar Borno shi kuma na Jahar Katsina Wanda akayi jana’izar mamatan dashi ne ya Tabba tarwa Jaridar Mikiya Adadin Mamatan.
Allah ya kawo mana Saukin wannan Al’amari.
Ahmed T. Adam Bagas