Labarai
Matsalar Tsaro:- Buhari yana Ganawa da Shuwagabannin Tsaron Kasar yanzu Haka.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yana jagorantar taro kan sha’anin tsaro a fadarsa da ke Abuja, a cewar mai taimaka masa kan shafuan zumunta.
Bashir Ahmad ne ya wallafa a shafinsa na Twitter ya ce hafsoshin tsaron kasar da sauran manyan masu ruwa da tsaki kan tsaro a gwamnatinsa na cikin mahalarta taron.
Sai dai bai yi karin bayani kan abubuwan da suke tattaunawa ba.
Ana wannan taro ne kwanakin kadan bayan gwamnan jihar Borno Babagana Zulum ya zargi jami’an tsaron kasar da yin zagon kasa a Sha’anin yaki da Boko Haram.
Zulum yayi wannan zargin ne bayan Harin kwantan bauna da Yan boko Haram, suka kai kan ayarinsa a kan Hanyar Maiduguri zuwa Baga.
Ahmed T. Adam Bagas