Tsaro

Matsalar Tsaro:- Gwamnatin Zamfara Ta Raba Motoci 200 ga Jami’an Tsaro.

Spread the love

A cigaba da yunkurinta na ganin ta kawo karshen matsalar tsaro da Ta Addaabi jahar.

Gwamnatin jahar Zamfara karkashin jagorancin Hon. Bello Muhammad Matawallen Maradun, yace ya kaddamar bayar da motocin ga dukkanin jami’an tsaron jahar Zamfara da su ka hada;-

‘Yan Sanda, sojojin Kasa, da na sama, Dss, da civil Defence, Hukumar Hana Shige da fice ta Kasa, Hukumar gyara Hali ta Kasa, da hukumar yaki Da cin hanci da rashawa, Da hukumar yaki da fataucin Miyagun kwayoyi Sai hukumar Hisba da kuma Zarota.

Da yake Jawabi Matawalle bayyana cewa raba wadannan motocin ya biyo bayan yunkurin Gwamnatinsa ne, na yaki da tada zaune tsaye a cikin jahar.

Haka zalika Gwamnan ya yi kira ga dukkanin masu tayar da kayar baya da basu aminta da sulhu da gwamnatin ba, da su yi gaugawar Mika wuya ga Tsarin Sulhun, Idan ba haka ba gwamnatin a shirye take domin yakarsu da Bakin Wuta kamar yadda Ya Fada.

Da su ke jawabi shuwagabannin dukkanin rundunonin tsaro Na Jahar Zamfara sun bayyana godiya ga gwamnatin akan irin goyon bayan da gwamnatin ke ba su tare da alkawarin cigaba da aiki tukuru domin Kare rayukkan Al’ummar jahar da dukiyoyinsu. Tare da godiya ga Gwamnan akan Dawainiyar da yake yiwa Sha’anin Tsaro.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button