Tsaro

Matsalar Tsaro:- Mata Sunyi Zanga Zanga kan Rashin Tsaro a Kaduna.

Spread the love

A Yau alhamis 23 ga watan Yulin, ne Matan a Kudancin Kaduna, sun shiga wata zanga-zangar nuna kyama game da kashe-kashen da ke faruwa a yankin, matan Sun Sanya Bakaken Tufafi, wasu Kuma sun Cire rigunan dake Jikinsu a Yayi Zanga Zangar

Kudancin Kaduna, wanda galibi Kiristoci sun fi Rinjaye a yankin, shi yayi fice wajen tashe-tashen hankula masu nasaba da kabilanci fiye da kowane yanki a Arewacin Najeriya.

Ko a ranar Lahadin da ta gabata, mutane 16 ne aka ruwaito sun mutu a wani hari da har yanzu ba a ga ‘yan bindigar ba.

Ana ci gaba da kashe-kashen duk da an tura tura jami’an soji zuwa yankin.

Ahmed T. Adam Bagas

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button