Tsaro
Matsalar Tsaro: Matasa Sun Bankawa Allo Mai Dauke Da Shugaba Buhari Da Masari Wuta A Katsina.
Da Safiyar yau Talata ne dai wasu Fusatattun matasa da suke gudanar da zanga zanga a garin Yan Tumaki dake karamar hukumar Danmusa Ta Jahar katsina suka Sanya wa Manya Alunan da ke dauke da Potounan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Gwamnan Jahar Aminu Bello masari wuta.
Masu zanga zangar dai sunce suna zanga zangar ne domin Irin Kisan kiyashin da yan Bindiga barayi shanu da garkuwa da mutane ke musu inda suke zargin Gwamnati taki daukar matakin da yadace na kawo karshen zubarda jini a Yankin Inji Su.
Daga Ahmed T. Adam Bagas