Matsalar tsaro mawaki rarara ya tura da Tallafin waka jiharsa ta katsina
Masalar Tsaro a Jihar Katsina: Rarara Ya Yi Tsokaci.
A karon farko fitaccen mawakin Siyasa Dauda Kahutu Rarara, ya tsoma baki tare da yin sabuwar waka game da halin rashin tsaro da yake addabar jihar Katsina.
Mutane da dama, dai sun dade suna so su ji abin da mawakin zai ce game da yanayin da al’ummar Katsina suka tsinci kan su na matsalar rashin tsaro a jihar kasancewar sa shi ma Bakatsine ne.
Inda har wasu suke ganin cewa Rarara ba zai iya cewa komai ba, ganin cewa Gwamnatin Apc ce, wadda ya ke yi waka ta ke mulki a jihar.
Wasu na ganin Kwata-kwata mawakin gum zai yi da bakin sa, ba zai iya nusar da gwamnati ba, game da kisan kare dangi da ake yi wa talakawa ba.
Ita dai wannan matsala ta tsaro a jihar Katsina ta fara ne a yankunan da ke zagaye da dajin rugu, wato Kananan hukumomi irin su, Safana, Faskari, Kankara, Batsari Jibiya, Dan Musa, Sabuwa da sauransu.
An dade ana kai komo tsakanin jam’ian tsaro da Fulanin daji don ganin an shawo kan matsalar amma abin ya ci tura. Har sai da ta kai ga Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari, ya yi tattaki tare da mukkaraban sa har zuwa inda wadannan Fulani suke domin yin sasanci da su a shekarar da ta gabata. Wanda a wancan lokacin suka sha alwashin aje makaman su tare da mika wuya da kuma daukar alkawarin cewa komai ya wuce.
Kwatsam kuma daga baya, sai Fulanin su ka yi burus da wannan sasancin, su ka ci gaba da kai hare-hare a kauyukan da abun ya shafa, wanda har yanzu ake ci gaba da asarar rayuka da kuma dukiyoyi wanda ba a san iyakar su ba.
A ranar Talata, 23 ga watan Yuni 2020 Rarara ya saki sabuwar wakar mai taken ‘Gwamnan Mu Masari Mai Hakuri’ wakar mai kimanin minti 15 da sakan 14 ta sha bamban da irin sauran wakokin da mawakin ya saba yi.
A wakar mawakin ya yi kira ga al’ummar jihar Katsina, da su hada kai babu batun dan Apc ko PDP, a cewar sa matsala ce da ta addabi kowa.
Haka kuma a cikin wakar ya bayyana cewa addu’a ce ya kamaci ace kowane Dan Jihar Katsina ya dage da yi don ganin cewa matsalar ta zo karshe.
Mawakin ya kara da cewa wannan annoba a dauketa a matsayin Kaddara, wadda kowa ke kan mulki zai iya fuskantar ta.
Bugu da kari a wakar ya ta nanata cewa babu abin da ya dami Gwamna Masari kamar wannan matsala ta tsaro, wadda kuma kullum bai da burin da ya wuce ya ga karshen ta.
Duk dai a cikin wakar Rarara ya kira ga Masari tare da jan hankalin sa, da ya kara zage damtse don ganin an kawo karshen wannan annoba.