Matsalar tsaro Nima nayi kuskure Haka a Lokacin Mulki na ~Inji Jonathan.
Tsohon shugaban kasar ya ce shi ma ya fuskaci kalubalen yayin da yake kan mulki, Ya kasance a wancan Lokacin akwai rashin tsaro da yawa. Don haka, ni mutum ne mai kuskure kan rashin tsaro a kasar a kuma Lokacin.
Ya yi magana ne a wani taron Umurni na Musamman na Commonwealth a Abuja, ranar Juma’a Jonathan Yace Abin da kawai za mu iya yi shi ne mu hada hannu mu mara wa gwamnati baya, mu karfafa wa sojoji da sauran jami’an tsaro gwiwa su kara kaimi don kare lafiyarmu, ”in ji shi.
Ya lura cewa rashin tsaro lamari ne na duniya kuma Najeriya don Haka ba wani abu ba ne saboda haka a karfafa matasa suyi amfani da baiwarsu wajen nuna hadin kan kasar.
Da yake amsa tambaya kan ko zai tsaya takarar Shugaban kasa na 2023, sai ya ce “takarar shugaban kasa a 2023 Lokaci ya yi wuri da za mu yi magana game da hakan. “
Wasu gwamnonin APC sun ziyarci tsohon shugaban a gidansa da ke Abuja kwanakin baya don bikin cikar sa shekaru 63.
Amma, majiyoyin kusa da taron sun bayyana cewa ganawar ta yi magana a siyasance kuma ba ta da nasaba da zaben shugaban kasa na 2023.
Hakanan, shugaban kungiyar gwamnonin masu ci gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi da gwamnan jihar Jigawa Badaru Abubakar sun ziyarci tsohon shugaban kasar a mahaifarsa.