Matsalar tsaro Shugaba Tinubu ya bukaci taimakon Sarakunan gargajiya domin cigaba da hako man fetir.
Shugaba Bola Tinubu ya bukaci hadin kan sarakunan yankin Neja Delta wajen wanzar da zaman lafiya da tsaro a yankin.
Tinubu ya ce hakan shi ne don tabbatar da yawan hako mai da habaka tattalin arzikin kasar.
Bola Tinubu ya bayyana hakan ne ta Bakin Ministan harkokin Neja Delta, Engr. Abubakar Momoh, wanda bayyana hakan a ranar Asabar a lokacin da yake jawabi a taron Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Jihar Delta a fadar Shugabansu, Mai Martaba, Manjo-Janar (Mai Ritaya) Felix Mujakperuo, Orhue I, Orodje na Masarautar Okpe.
Wadanda suka halarci taron sun hada da mataimakin shugaban majalisar, Pere na Akugbene Mien, Luke SP Kalanama VIII; the Ovie of Oghara Kingdom, Noble Eshemitan, Uku Oghara N’ame, Orefe III; Ovie of Idjerhe Kingdom, Mai Martaba Monday Whiskey, Udurhie I; Ovie na masarautar Abraka, Luke Erede Ejohwomu, Adakaji; da kuma Osuivie na Masarautar Agbarho, Mai Martaba Samson Owheriijesu Ogugu I, da dai sauransu.
Momoh ya lura cewa jihar ta zama jiha ta shida da ya kai ziyara wajen isar da sakon shugaban kasa a fadin yankin Neja Delta.
A cewarsa, gwamnati mai ci tana girmama sarakunan gargajiya “kasancewar masu kula da zaman lafiya a kowace al’umma”.
Ya ce, “Mun zo nan ne domin mu ba ka sakon fatan alheri na mai girma shugaban kasa, Sanata Bola Ahmed Tinubu. Kuma ya bukaci da na yi kira ga sarakunan gargajiya da su taimaka wajen wanzar da zaman lafiya a wannan yanki ta yadda za a samu yawan man fetur, da kuma habaka tattalin arzikin kasa.”
Ministan ya bayyana cewa gwamnati ta san cewa “Nija Delta wuri ne mai cike da tashin hankali”.
Kuma domin mu bunkasa tattalin arzikin Najeriya, dole ne yankin Neja Delta ya kasance cikin zaman lafiya. Kuma zaman lafiya da tsaro na daga cikin manyan abubuwan da shugaban kasa ya sa a gaba kamar yadda yake kunshe cikin manufofin sa.
Kuma domin mu samu zaman lafiya da tsaro, ko shakka babu sarakunan gargajiya da gwamnonin jihohi za su taka rawar gani sosai. Shi ya sa muka zo yau (Asabar) muka fara daga ofishin Gwamnan Jihar domin idan ana maganar masu ruwa da tsaki a kowane yanki sai ka yi maganar Gwamnan Jihar ka san cewa sarakunan gargajiya ne. na gaba ta fuskar matsayi,” inji shi.