Tsaro
Matsalar Tsaro;- Sojoji Najeriya 127, ne Zasu Ajiye Aikin su.
A watan Maris Mai Zuwa ne, Sojojin Kasar Nan guda 127, ne zasu bar aiki a gidan Soja.
Sojojin Sunce zasu bar aikin ne bisa Ra’ayinsu Na Karan Kansu.
Shugaban Sojin Najeriya Laftanar Janar Tukur Burtai, ya Amince da Barin aikin Nasu.
Burtai yace zuwa watan Maris lokacin Sallamarsu zayi kamar yadda kundin tsarin gidan Soja ya tanada.
Sai dai a Baya bayan nan Kananan Sojoji a Najeriya suna kokawa da Rashin Kayan Aiki yadda ya kamata wanda dalilin haka ya sanya ‘yan Ta’adda ke samun galaba a Kansu a wasu lokutan, Sai dai wasu Manyan Sojoji suna Musanta Irin wannan Kalaman.
Masu karatu ya Kuke kallon Ajiye Aikin Matasan Sojojin a Dai dai lokacin da Kasar Nan Ke Fama da Matsalar Tsaro????
© Ahmed T. Adam Bagas