Matsalar Tsaro: Zulum ya gana da Sojojin ruwa,da na Sama a Abuja
Daga Ahmed T. Adam Bagas
A wani bangare na jerin shirye-shiryensa na ziyarar aiki yau Talata a Abuja, Gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum ya gana da Babban Hafsan Sojan Sama, Mataimakin Admiral Ibok Ekwe Ibas da shugaban Hafsin Sojan Sama, Air Marshal Sadique Baba. Abubakar.
Taron daban, wanda aka gudanar a hedikwatar sojojin sama da hedkwatar sojojin ruwa a Abuja, sun tattauna matsalolin tsaro a jihar Borno.
A lokacin da Zulum ya ke gabatar da kokensa ga Rundunar game da ta tura karin sojojin ruwa zuwa Borno. Ya bayyana sojojin ruwan Najeriyar a matsayin wani muhimmin sashi na yakar ayyukan Boko Haram a gabar tafkin Chadi.
Gwamnan ya yaba wa rundinar sojin ruwa a kan kokarin da suke yi a kokarinsu na yakar ayyukan ta’addanci a arewa maso gabas.
Da yake mika bukatarsa ga Rudunar Sojan Ruwan, Zulum ya nuna himmar gwamnatin Tarayya na sake fasalin hanyar da ta hada hanyar Baga zuwa gabar tafkin Chadi, don saukin ayyukan jami’an tsaro da al’ummomin da suka dawo.
Yayin da yake a hedikwatar rundunar ta Sojan Sama, Zulum ya kasance cike da yabo ga Hafsan Sojan, yana mai jaddada cewa sansanin sojojin a Maiduguri ya amsa duk bayanan sirrin da suka mika musu Inji Zulum.
Da yake mayar da martani, Mataimakin Air Marshal Sadique Abubakar ya sake nanata kudirinsu na yakar ‘yan tawaye a jihar Borno.
Air matshal Sadique ne ya jagoranci gwamnan a sashin lura da hedikwatar Sojan Saman.