Tsaro

MATSALAR TSARO…..

Spread the love

Daga Mutawakkil Gambo Doko

Yankin Arewacin Najeriya ya faɗa matsalar tsaro tun daga shekarar 2010 zuwa yau wato a taƙaice an kwashe shekara 10 ana kashe bayin Allah da basu ji ba basu gani ba a sassa daban-daban a yankin. Duk da kasancewa a cikin waɗannan shekaru 10 an samu chanjin gwamnatoci har guda uku wato gwamnatin Marigayi Umaru Musa Yar’adua, Dr. Goodluck Ebele Jonathan da gwamnatin shugaba mai ci a yanzu wato Shugaba Muhmmadu Buhari . Wani abin mamaki, A wannan gwammatin yawanci duk wani babban muƙami a fannin tsaro zaka ga ɗan Arewa ne yake riƙe dashi amma har yanzu bata chanja zani ba. Sakamakon haka nayi kwarya-kwarya nazari dangane da matakan dayakamata gwamnati ta ɗauka domin ɗakile wannan matsalar:

1- GARANBAWUL GA MANYAN JAMI’AN HAFSOSHIN TSARO

Matakin gaggawa dayakamata gwamnati ta ɗauka shine tayi garanbawul ga manyan hafsoshin jami’an tsaron ƙasar kama daga kan ministan tsaro, mai baiwa shugaban ƙasa shawara a fannin tsaro, shugaban jami’an sojin ƙasa, sama, ruwa da shugaban rundunar ƴan sanda, kwastam, immigration da sauransu domin sun gaza wajan kare rayukan al’ummar Arewacin Najeriya. Wannan kuma shine abin da Hon. Faruƙu Adamu Aliyu ya bayyana a wata hira da suka yi da gidan rediyon Bbc-Hausa a cikin shirin ra’ayi riga a ranar 31/5/2019 wanda ya bayyana cewa sunyi magana baki da baki da shugaban kasa akan za’a chanja ɗaukacin manyan hafsoshin jami’an tsaron ƙasar saboda basirarsu ta ƙare wajan magance matsalar tsaro a ƙasar. To muna tunawa Shugaban ƙasa a ina aka kwana akan wannan batun?

2- WA’ADI

Dole ne sababbin manyan hafsoshin tsaron da za’a naɗa su zama kwararru a fannin saro sannan a basu wa’adi na magance wannan matsalar ta tsaro cikin gaggawa sannan kuma a tursasa musu zama a jahohin da ayyukan ƴan ta’adda suka yi ƙamari har sai an kawo ƙarshen matsalar. Harwayau, shugaban ƙasa ya zaɓi wakili amintacce wanda zai ke kawo musu ziyarar ba zata domin ganin yadda suke gudanar da al’amuransu. Ko shi shugaban ƙasa tare da haɗin gwiwar gwamnoni suke zuwa da kansu

3-SAMARWA DA SOJOJIN KAYAYYAKIN YAƘIN ZAMANI

Babu yadda za’ayi ƴan ta’aɗda suna amfani da manyan makamai wajan kai hare-hare su kuma sojojinmu suna amfani da ƙananan makamai a kawo ƙarshen matsalar tsaro. Dan haka gwamnati ta samar musu da ingatattun kuma wadatattun kayayyakin yaƙin zamani. Sannan ta kyautata albashinsu da basu alawus akai-akai. Bugu da ƙari, tayi ƙoƙarin chanja musu a wuraren aiki duk bayan wata shida ko ƙasa da haka domin gudun kada cin hanci da rashawa ya mamayesu

4 – HAƊIN GWIWA DA SARAKUNAN GARGAJIYYA

Gwamnati ta zauna da sarakunan gargajiya a teburin shawara dangane da wannan batun domin su ma suna da gudunmawar da zasu iya bayarwa. Amma wani hanzari ba gudu ba gwamnati ta zu ba ido duk wani sarkin ko mai sarautar da aka tabbatar yana taimakawa ƴan ta’adda a cire masa rawaninsa nan take tare da hukuntashi domin ya zama darasi ga ƴan baya

5- YAƘI DA FATARA DA TALAUCI

Wajibi ne gwamnatin tarayya dana jahohi su tashi tsaye wajan yaki da fatara da talauci a ƙasar domin rashin aikin yi yana taimakawa matasanmu wajan faɗawa ayyukan ta’addanci. Sannan a hannu ɗaya, Gwamnati ta ɓullo da wani shiri na musamman a makarantu da gidajen yaɗa labarai wanda zai kinsawa matasanmu kishin ƙasarsu da al’ummarsu

6- ADDU’A TAKOBIN MUMINI

Dole sai al’umma mun duƙufa wajan gudanar da addu’o’i babu dare babu rana wajan roƙon Allah ya kawo mana ƙarshen matsalar tsaron da take addabarmu.

RanarArewa2020

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button