Labarai

Matsin tattalin Arzikin da Nageriya ta afka ba Mai jumawa bane~Zainab Shamsuna

Spread the love

Ministar, Kasafin Kudi da Tsare-tsaren Kasa, Zainab Ahmed, ta ce koma bayan tattalin arzikin Najeriya na dan karamin lokaci ne; tana mai bayar da tabbacin cewa kasar ba da daɗewa ba za ta fita daga koma bayan tattalin arziki a farkon rubu’in shekarar 2021.

Ministan ta bayar da wannan tabbaci ne a taron koli na Tattalin Arzikin Nijeriya karo na 26 wanda Kungiyar Taron Tattalin Arzikin Najeriya da Ma’aikatar Kudi, Kasafin Kudi, da Tsare-tsaren Kasa suka shirya ayau ranar Litinin a Abuja.

Ministan ta lura cewa annobar COVID-19 ta haifar da koma bayan tattalin arziki a Najeriya yanzu. Misis Ahmed ta ce koma bayan tattalin arzikin ya biyo bayan yadda aka saba a duk duniya inda kasashe da dama suka shiga matsalar tattalin arziki saboda annobar.

Misis Ahmed ta ce “Najeriya ba ita kadai ba ce a cikin wannan, amma zan ce Najeriya ta zarce dukkan wadannan tattalin arzikin ta fuskar Sakamakon bincike.

Ku tuna cewa a ranar Asabar din da ta gabata Najeriya ta fada cikin matsin tattalin arziki na biyu cikin shekaru biyar.
Alkaluman Hukumar Kididdiga ta Kasa, NBS, sun ce tattalin arzikin Najeriya ya ragu da -2.48%.

NBS ta bayyana cewa koma bayan tattalin arziki shine mafi munin da Najeriya tayi cikin shekaru da dama.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button