Mawaki Rarara ya bukaci Kotu da tayi watsi da tuhumar da wani dan kasuwa ke masa na cewa yana binsa bashin milyan Goma 10m.
Ana tuhumar Rarara ne da rashin biyan kudi sama da Naira miliyan 10 ga wani dan kasuwa, Muhammad Ma’aji.
A zaman da kotun ta ci gaba da zama a Rijiyar Zaki karkashin jagorancin mai shari’a Halhalatul Khuza’i Zakariyya, lauyan Rara, G. A. Badawi, ya shaida wa kotun cewa shari’ar ba ta da tushe don haka a yi watsi da ita.
Ya kara da cewa sun bayar da amsarsu a rubuce ga koke-koke da kotu, amma masu gabatar da kara sun yi ikirarin cewa sun samu a makare ne a lokacin da kotun ta kusa zama.
Wanda ya shigar da karar, Muhammad Ma’aji, ya shaida wa kotun cewa yana da dukkan shaidun da aka rubuta a rubuce don tabbatar da ikirarinsa tun farkon dangantakarsa da Rara a shekarar 2021 amma bai samu ko sisi ba.
Mai shari’a Halhalatul Khuza’i Zakariyya ta umurci lauyan da ke kara da ya mayar da martani ga lauyan da ake kara da kuma kotun a rubuce.
Mai shari’a Zakariyya ya dage sauraron karar zuwa ranar 12 ga watan Mayu domin ci gaba da sauraron karar.