Mawaki Rarara ya sa gasar mota a wakar Nageriya
Fitaccen Mawakin Siyasa, Dauda Kahutu Rarara ya sanyawa mawakan Hausa na gargajiya, da na zamani gasar yi wa kasar Nijeriya sabuwar waka.
Rarara ya bayyana haka ne, jim kadan bayan lafawar zanga-zangar da wasu ‘yan kudancin Nijeriya su ka yi, ciki har da fitattun mawakan su don ganin rushe rundunar ‘yan sanda ta SARS.
A Bangaren Rarara shi kuma sai ya bukaci Mawakan na zamani da na gargajiya da su rera sabuwar wakar Nijeriya wadda ta shafi zaman lafiya a kasar baki daya.
Don a bayyanawa Jama’a muhimmancin hadin kai, wanda kuma duk inda babu hadin kai to, babu zaman lafiya.
A hirar sa da kafar watsa labarai ta Kannywood Exclusive, Rarara ya ce, wannan dama ce ga mawaka ‘yan uwana kowa ya gwada irin kaifin basirar da Allah ya yi masa, don ganin ya wake kasar nan, sannan kuma fahimtar da al’umma cewa ba mu da kasar da ta fi Nijeriya don haka sai mun son junan mu, mun cire kabilanci babu batun dan Arewa ko dan kudu.
Hakan yasa muka raba gasar Rukuni kashi uku.
Rukuni na Farko, shi ne Mawakan Gargajiya, irin masu wakokin Asharalle, masu Kukuma, har ma da masu kacaukara duk za su iya shiga gasar.
A cikin wadanda suka shiga gasar, za mu tantance mutane 10 wadanda wakar su ta fi ma’ana, mu basu kyaututtuka. Na farko za a ba shi, mota, na biyu zai samu Adaidaita Sahu, na uku kuma za mu ba shi sabon mashin, sauran mutane 7 za mu ba kowa naira dubu dari da hamshin hamsin.
Rukuni na biyu kuma su ne Mawakan Zamani, masu wakokin soyayya da na Siyasa, su ma za a ware mutum 10, wanda ya zo na farko za a ba shi mota, na biyu Adaidaita Sahu, na uku sabon mashin, sauran mutane bakwai, su ma za a ba kowanen su Naira dubu dari da hamshin hamsin.
Rukuni na uku su ne, masu yin dan gajeren bidiyon na Barkwanci (Comedy) su ma za su iya shirya Comedy ba mai yawa ba, jigon labarin ya kasance za a nuna muhimmanci zaman lafiya da kuma kishin kasar Nijeriya, su ma za mu basu irin kyaututtukan da mu ka ba mawaka.
Allah ya ba mai rabo sa’a.