Labarai

Mawaki ya Roki Jama’a da su saka Baki tsakanin aurensa da matarsa

Spread the love

Mawaki Abolore Adegbola Akande wanda aka fi sani da 9ice, ya fito ya roki jama’a da su taimaka masa su roka Masa matar sa afwa Olasunkanmi, bayan bidiyon da ya dauka tare da wata mata a wani otal da Wanda ya shiga yanar gizo.

A cikin makon, bidiyon mawaƙin da wata baiwar Allah sun yi ta zagawa. 9ice ana iya ganinsa yana lallashin matarsa kuma yana gargadin wasu samari dasu nisance ta. Hakanan an yada hoton shi tsirara a

Wani Mai suna sober 9ice ne ya yada bidiyo a shafinsa na Instagram a yammacin jiya asabar yana rokon jama’a da su taimaka masa su roki matar tasa wacce ya aura a watan Janairun 2020.

A cikin bidiyon, mawaƙin ya ce wannan shi ne aurensa na uku kuma yana son wannan auren ya dore

“ Na aikata wani abin kunya, wani mummunan abu kuma ya bata min iyalina kuma abu mafi muhimmanci a wurina halin yanzunnan.

9ice din da kuke gani koyaushe kuma yake damuna shine saboda ina da kashin baya, Olasukanmi Akande kuma saboda wannan mummunan aikin da na aikata, yana ci min tuwo a kwarya.

Ina neman afuwa kan abinda nayi kuma ina bukatar ku maza ku taimaka ku roki matata. Ita ce kashin baya na.

Na yi fice a cikin wasu abubuwa da yawa amma abu daya da nake kasawa shi ne aurena amma wannan auren, ina so ya yi aiki. Don Allah, taimake ni ka roƙi matata. Ajiye min wannan auren ” in ji shi. Ku Kalli bidiyon

https://www.instagram.com/p/CH26G8BDtZ5/?igshid=j4c75gou4h3x

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button