Labarai

Mawakiya Dija tace bazata lamunci zagin rahama sadau ba

Spread the love

Mawakiyar Dija ta gargadi wata mai bin ta da ake kira Abdulrahman illo da yin amfani da rayuwarta wajen cin mutuncin wani.  sun fara wannan dambarwa ne lokacin da illo yayi share din maganar Dija zuwashafinsa na Twitter don bayyana kamannin rayuwar mawakiyar. A cewarsa, yana son rayuwa irin ta dija a gaskiyar cewa waka bata hana Dija aure ba, ba kamar irin ‘yar wasan kwaikwayo Rahama Sadau. Da dayake magana a kan jarumar , illo ya ce rahama sadau ba ta tunanin aure. Sai ita kuma Dija  ta ce wa mai bibiyar kada ka yi amfani da rayuwarta don cin mutuncin wani. A cewarta, kowa yana da yadda yake so yayi rayuwa kuma tsarin Allah ne mafi alkhairi. Ta lura cewa ba za ta lamunta da duk wani kalaman batanci ga ‘yar wasan ba, yayin da ta gargadi mabiyanta da su girmama juna.
daman dai ita Jaruma Rahama sadau kawace ga mawakiyar dija domin kuwa film din Mati a zazzau da Rahma ta dauki Nauyin sa saida ta gayyato dija mawakiya ta saka a ciki, Dija dai shahararriyar mawakiya ce da harshen turanci da hausa…

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button