Mayakin Boko Haram Sa’ad Karami Ya Zubar Da Makamansa Ga Sojojin Najeriya..
Daga Miftahu Ahmad Panda.
Malam Adamu Yahaya (Wanda Akafi Sani Da Saad Karami), ya Bayyana Cewar yayi Saranda Tareda Zubar Da Makamansa Ga Bataliyar Sojojin Najeriya Ta 242 a Mungono ne Bisa Radin Kansa.
A nata Bangaren Rundunar Sojojin Najeriya Ta Bayyana Cewar Sunyi nasarar Kama Saad Karami ne a wani Sumame data Gudanar a Garin Baga, Inda tayi nasarar Dakumoshi a Harin Da Sukakai.
A jawabin Da Ko’odinetan Rundunar Tsaro, Manjo Janar John Enenche ya Fitar Yabayyana Cewar Saad Karami Yanada Daga Cikin ‘Yan Bindigar Da Sukakai Hari Garuruwan Metele, Mairari, Bindiram, Kangarwa dakuma Garin Shetimari dake Kasar Jamhuriyyar Nijar,
Adamu Yahaya Dai ya Mika Wuya Ga Rundunar Sojojin ne a Wannan Makon Ranar 24 Ga Wannan Wata na Mayu damuke Bankwana Dashi.
Ko’odinetan yakara Dacewar Sojojin sun Samu Wannan Nasarar ne Bisa Luguden Aman Wuta Da Sukayiwa Yankin, Kafin daga Bisani suyiwa Sashen Da ‘Yan ta’addan Suke Kwanton Bauna.
Yakara Dacewar Jami’an Sojojin Camp 11 dake Gambouru karkashin tawaga ta Farko a rundunar Operation Lafiya Dolene Suka Samu Nasarar Dakumo Matashin Dan ta’addan Bayan Da Dubunsa Ta Cika.
Sannan a sumamen Da Rundunar Takai Garin Mudu na Jihar Borno, Rundunar Tayi Nasarar kashe Mayakan Boko Haram Guda 12, Tareda Samun Mutum 241 wadanne ‘Yan ta’addan Suka kame, Mutanen sun Hadarda Mata 105 dakuma Kananan Yara 136.
Wasu Daga Cikin Kayayyakin Da Rundunar Tayi Nasarar Hafzi Dasu sun Hadarda Tutoci Guda 4, Mashin Guda 1, Dakuma Keke Guda 2, Sai Na’urar Sauti Ta Ample Fier Guda Daya dakuma Keken Dinki Guda 2.
Haka Zalika Enenche Yabayyana Cewar ba’a Samu Asarar Rai Ko Dayaba a Sumamen Da Rundunar Sojojin Takai.