Labarai

MDD Ta Bukaci A Gudanar Da Bincike Kan Cin Zarafin Masu Zanga zanga A Amurka.

Daga Haidar H Hasheem Kano

Babban Maga Takarda na Majalisar dinkin duniya Antonio Guterres ya bukaci a gudanar da bincike kan cin zarafin masu zanga zanga da Yansa suke yi a kasar Amurka, ya kara da cewa dole ne zanga zanga ta kasance ta luman, ita kuma hukuma dole ne ta nuna sanin ya kamata wajen tunkararsu a kasar Amurka ne ko ma a ko ina a duniya,

Ana sa bangaren mai Magana da yawun babban maga takardar majalisar dinikin duniya Stephen Dujjaric da yake bayani ga manema labarai a babbar hedkwatar majalisar dinkin duniya dake birnin New York ya bayyana cewa a ‘yan kwanakin nan mu shaida yadda yan sanda ke ci zarafin masu zanga zanga a kasar Amurka inda aka ta yin awon gaba da masu zanga zanga a kowanne dare tun daga ranar laraba da ta gabata, kuma suna zanga zangar ne domin nuna bacin ransu game da kisan gillan da Yan sanda suka yi wa wani bakar fata mai suna Gorge Floyed a Garin Minneapolis a makon jiya.

Har ila yau ya bayyana cewa Gutteres ya nuna damuwarsa sosai game da harin da Yan sanda suka kai wa ‘yan jarida a lokacin zanga zangar da ta yadu a biranen kasar ta Amurka, da hakan ya jawo ta da zaune tsaye da kone kone da sace dukiyar jama’a, kai hari kan yan jaridu da sauran jama’a lamarin ne mai muni , saboda Demkuradiya ba za ta yi aiki ba idan babu yanci yan jaridu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button