Me Ake Nufi Da Beli (Police Bail)? Doka Ta Yarda Da Amsar Kudin Beli Da ‘Yan Sanda suke Yi?
Me ake nufi da BELI (Bail)
Beli ko Bail da turanci kuma a idon doka yana nufin wani hanya ne da zai bada damar a saki wanda ake zargi ko ake chajin shi da aikata wani laifi daga ita hukumar da ta tsare shi, akan sharadin zai bayyana a gaban kotu ko police station a duk lokacin da suka bukaci hakan.
A Nigeria muna da Beli iri biyu ne kamar haka:
1-Police or Administrative Bail
2-Court Bail
Amma zanyi magana ne akan Police Bail.
Wannan Police Bail wani kalan Beli ne da ake ba da shi ga wanda ake zargi da aikata wani laifi.
A wannan gaba jami’an ‘yan sanda ko wata cibiyar bincike ta gwamnati da take bincikar abunda ya faru to bata gama tabbatar da cewa ya aikata laifin ko bai aikata ba, to sai ta bada belin sa dan gudun karya wata dokar kuma. Atakaice bata gama tattara dalilan da zasu iya sanyawa ta chajeshi dasu a kotu ba.
To amma kuma ga dokar kasa tace duk mutumin da aka tsare dan ana zargin sa da aikata wani laifi to dole a kaishi kotu a cikin awa 24, idan ya zama a kusa da police station din akwai kotun da take da hurumin da za ta saurari wannan karar wanda ya zama nisan kotun da police station bai haura kilometers 40 ba; inda kuma ya zama tsakanin kotun da ofishin ‘yan sanda ya haura nisan kilometres 40, to wanda ake zargi dole a kaishi kotu a cikin awa 48 kamar yadda doka ta tanada.
Saboda haka haramun ne a dokar kasa, kuma ya saba da doka ace ‘yan Sanda ko wasu cibiyoyin bincike na gwamnati su tsare wanda ake zargi da aikata wani laifi har na tsawon kwana biyu (48hrs) ba tare da sun bada belin sa ba ko kuma sun kai shi kotu ba.
Wadannan hukumomin sun hada da: hukumomin yaki da cin Hanci da rashawa na EFCC, ICPC, NDLEA da sauran su.
TO DOKA TA YARDA DA AMSAR KUDIN BELIN DA MAFI YAWAN JAMI’AN ‘YAN SANDA SUKE YI ?
Alal hakika doka bata yarda ba kuma bata sahale ma kowanne Jami’in dan sanda ya amshi kudin beli ba domin kuwa kyauta ne, amsar kudin ya saba ma doka ta kowane fuska.
Amma yanzu mafi yawa daga cikin jami’an ‘yan sandan ba zasu bada belin ka ba har sai ka biya kudin belin tare kuma yin hakan ya saba ma doka, idan kace masu ai kyauta ne, amsar kudin bashi a cikin doka sai suce ai ba kudin beli bane wannan kudin ajiyeka da gadin ka da sauran su ne da akayi, wannan dama sauran wasu dabaru, idan ka nuna ba zaka bada ba to zasuyi barazanar rike ka kuwa, wanda kuma hakan ya saba da doka ta kowanne fuska.
Dan haka idan har hakan ta faru dakai zaka iya kai karar su ta wadannan Hanyoyi kamar yadda hukumar yan sanda ta kasa ta sanar:
Kira:
08057000001
08057000002
WhataApp:
08057000003
Bissalam
Shehu Rahinat Na’Allah
10th August, 2020.