Rahotanni

Me Yasa Kullum Wa’azi Sai Akan Talaka Yake Ƙarewa A Najeriya?

Spread the love

A Haƙiƙa a bisa nawa mizanin fahimtar kafin a samu talakan da ya kai na Najeriya haƙuri, kawaici, juriya da ma yafiya dangane da abubuwan da ake yi masa sai an kai ruwa rana. Misali:

1- Shugaba zai cuci talakawa a Najeriya ya kwashe kuɗaɗensu ya azurta kansa da ƴaƴansa, amma da zarar ya kamu da wata rashin lafiya ko ya mutu zasu shiga masallatai da coci suna yi masa addu’o’i nagari.

2- A Najeriya ne zaka ga shugaba ya yi fafa-lolo da dukiyar ƴan kasa, amma da zarar ya faɗa hannun jami’an tsaron ƙasar talakawa zasu fara bayyanawa tausayinsu agareshi tare da nuna rashin jin daɗinsu abin daya faru dashi.

3- Duk irin ƙuncin da talakawa suke ciki a Najeriya basa fasa yiwa shugabanninsu da ƙasarsu addu’o’in zaman lafiya da cigaba mai ɗorewa.

4- Ina da yaƙini da yadda talakawa a Najeriya suke tausayawa shugabanni haka suma suke tausaya musu, da yanzu ya sharɓi roman demokaradiyar da ake yi masa ƙarya shekara da shekaru

5- Talakan Najeriya duk azaɓar yake sha a mulki daban-daban amma bai taɓa boren daya haifar da kifar da wata gwamnati ba a ƙasar a tarihi, saɓanin waɗansu ƙasashen kamar na Larabawa da Turawa shugabanninsu suna kyautata musu amma kullum a cikin nuna gajiyarsu suke da bore ko kira ga juyin juya hali.

6- Talaka a Najeriya shekara da shekaru ana yi masa alƙawarin samar masa wutar lantarki, ruwan sha, hanyoyi, asibiti amma har yanzu ba a cika masa wannan alƙawarin ba ɗari bisa ɗari. Amma duk da haka bai fasa zaɓar shugabanni ba

Amma abin mamaki duk da haka, sai kaji waɗansu suna ikrarin talakawan Najeriya basu da hali

Daga Mutawakkil Gambo Doko

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button