Labarai

Mijina ba da tsafi yake aiki ba ya karbi mulkin Nageriya ne bayan Nageriya ta lalace ba zai iya gyarata a karamin lokaci ba ~Cewar Remi Tinubu.

Spread the love

Uwargidan shugaban Najeriya, Remi Tinubu, ta ce mijinta, Shugaba Bola Tinubu, na aiki tukuru don gyara kasar da ya gada bayan ta lalace, tana mai jaddada cewa shugaban kasar ba masihirci ba ne da zai gyara abubuwa cikin karamin lokaci.

Abin da muka gada shi ne abubuwan da suka faru shekaru da yawa da suka gabata; ba mu zo nan don dora wa kowace gwamnati laifi ba, sai dai mu gyara abin da ya lalace,” inji Misis Tinubu. “Mijina ba mai sihiri ba ne; zai yi aiki kuma na yi imani da fatan za mu samu zaman lafiya a kasar nan; mafi alheri har yanzu ya zo mana.”

Uwargidan shugaban kasar ta bayyana hakan ne a wurin taron coci-coci na mabiya addinai daban-daban domin tunawa da cikar Najeriya shekaru 63 da samun ‘yancin kai a ranar Lahadi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button