Ministan harkokin cikin gida Tunji-Ojo na da alaka da badakalar N438m ta Betta Edu
Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, yana da alaka da kwangilar N438M da tsohuwar ministar harkokin jin kai, Betta Edu ta bayar ga kamfanin New Planet Project.
Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, an alakanta shi da kwangilar N438M da tsohuwar ministar harkokin jin kai, Betta Edu ta bayar ga kamfanin New Planet Project, wanda ministan cikin gida ya kafa a shekarar 2003.
Ministan wanda aka gani a fadar shugaban kasa a ranar Talata, ya tabbatar da mallakar kamfanin a gidan talabijin kai tsaye, inda ya bayyana cewa ya yi murabus daga mukamin darakta a kamfanin a shekarar 2019. Sai dai kungiyoyin farar hula sun yi kira da a dakatar da ministan, saboda sabawa aikin gwamnati da dokoki.
Kudaden da aka ce an biya wa kamfanin da Ministan ya kafa sun hada da, Naira miliyan 279 don tantance wadanda suka ci gajiyar rajistar jama’a ta kasa da kuma karin Naira miliyan 159 don wannan manufa. Kamfanin, wanda aka yiwa rajista a ranar 3 ga Maris, 2009, har yanzu akwai Ministan da matarsa, Abimbola, a cikin gidan yanar gizon CAC a matsayin daraktoci. Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, a shekarar 2020, ya bayyana ministan harkokin cikin gida wanda a lokacin ya kasance dan majalisa kuma shugaban kwamitin majalisar wakilai na NDDC a matsayin daya daga cikin ‘yan majalisar dokokin kasar da suka ci gajiyar kwangilar NDDC da dama.