Ministar Kuɗi Zainab Ahmed Ta Bayyana Babbar Matsalar Da Take Hanata Bacci A Najeriya.
Ministar kudi, Zainab Ahmad, ta ce matsala ta farko da ke damunta ita ce ‘haraji’, ta biyu ‘haraji’, haka ma ta uku ita ce ‘haraji’
A cewar ministar, matsalar zirarewar haraji ta na hanata bacci da ido biyu a bude.
Zainab ta bayyana hakan ne yayin da ta ke amsa tambayoyi a wurin wani taro da aka yi domin murnar cikar Najeriya shekaru 60 da samun ‘yanci.
Zainab Ahmad ta amsa tambayar da Poju Oyemade, babban Fastoa cibiyar alƙawarin kirista (covenant christian church) yayin gudanar da wata tattaunawa da aka shirya domin murnar zagayowar ranar samun ƴanchin-ƙasa.
A yayin da aka tambayeta abubuwa uku da suke hanata bacci sai ministar tace; ”Abu na farko shine haraji, na biyu ma haraji, hakama na uku haraji.”
Sai dai, Ministar ta ce ma’aikatar ta na aiki tuƙuru don ganin ta yaƙi ƙaranchi da zirarewar haraji, wanda hakan ke hana samun isassun kuɗin-shiga ga ƙasa.
Ta cigaba da cewa; ”ma’aikatata ta fara amfani da hanyoyin fasahar zamani don ganin an samu daidaito a tsarin karba da tattara haraji na ƙasa.
Mu na yunƙurin hana zirarewa da kuma inganta haɗinkan mutanenmu, musamman dangane da tsarin karba da tattara haraji. Mun kawo sa hannun jari a tsarin sadarwa na zamani, sannan kuma mu na yunƙurin ganin tattara abubuwa wuri guda.
Muna da tsarin zama duk wata mu bibiyi tsarin harajinmu sannan mu tattara alƙaluma. Mu na aiki domin ƙara sanin duk wasu hanyoyin zamani da za su ba mu ikon ganin biyan harajin kamfanoni akai-akai ko in lokaci ya kusa.
Ministar ta ce Nigeria ta samu gagarumar nasara da kuma cigaba ta ɓangaren wadata kanta da abinci.
“Munayin duk iyakacin ƙoƙarinmu don mu tabbatar ƙasarmu ta wadatu kwarai, musamman a ɓangaren kayan masarufi da sauran kayan abinci” a cewar Zainab Ahmad
Sanna ta kara da cewa; dole na sanar da cewa mun samu gagarumar nasara a wannan ɓangaren, saboda ba don mun wadatu da abinci ba a lokacin kulle, da babu shiga, ba fita a ƙasa, da mun faɗa cikin gagarumar matsala.
Daga Comr Haidar Hasheem Kano