Labarai

Ministocin Tinubu ba za su iya ganinsa ba, haka mu ma ba za mu iya ganinsa ba – Ndume

Spread the love

Sanata Ali Ndume mai wakiltar Borno ta Kudu ya ce babbar matsalar da ke fuskantar su ita ce tsarin da ake zargin gwamnati na rufa-rufa, inda har wasu daga cikin ministocin Tinubu ba sa ganin Shugaban kasa, har da ‘yan majalisar da ke da niyyar ganinsa domin su tattauna batutuwan da suka shafi mazabarsu.

Sanata Ndume ya kuma yi gargadin cewa matukar ba a dauki matakin yaki da matsalar yunwa da ke yaduwa a kasarnan ba, matsalar karancin abinci mai gina jiki za ta addabi jama’a da dama a Najeriya kuma ta riga ta kama kananan yara a yankin Arewa maso Yamma.

A cikin hirar da BBC Hausa ta yi da shi a ranar Laraba, Sanatan ya ce rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadin cewa ‘yan Najeriya miliyan 82 za su gamu da yunwa da rashin abinci ba nan da shekaru 5 masu zuwa.

A cewarsa, “muna fargabar wata rana mutum zai je kasuwa da kudi ya fuskanci yanayin da ba za a samu abincin ba.”

Ya ce “muna da labari daga Katsina. Idan yunwa ta ci gaba, yara za su sha wahala sosai, yara ba su da abinci don ci gaba mai kyau. Wannan lamari ne da za ka samu a wuraren da ake fama da yaki ko yunwa. Mun ga yadda lamarin ya faru a Nijar da Sudan ta Kudu inda yara suka mutu. Yanzu haka lamarin ya kara tabarbarewa a Najeriya.”

Ya nuna damuwarsa cewa a da, gwamnati tana adana abinci a Bankin Abinci don bukatun gaggawa, amma yanzu babu. “Wannan lamari ne na matukar damuwa kuma ya kamata a yi wani abu da sauri game da shi,” in ji shi.

Da aka tambaye shi dalilin da ya sa ba zai iya ganawa da Shugaban kasa ya yi magana da shi a kan irin wadannan batutuwa ba a asirce maimakon ya yi magana da manema labarai, Sanata Ndume ya yi zargin cewa abu ne mai matukar wahala a yanzu domin “har wasu Ministoci ba sa iya ganin Shugaban kasa. “

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button