Nishadi

MU LEƘA BOLLYWOOD: Shin Ko Kun San Dalilin Da Ya Sa Har Yanzu Salman Khan Bai Yi Aure Ba?

Spread the love

Cikakken sunansa Abdul Rashid Salim, sunan mahaifiyarsa Salma(shi yasa ake kiransa da Salman Khan). An haife shi a ranar 27 ga Disamba 1965.

A tarihin Salman Khan ya yi soyayya da ƴan mata da yawa cikinsu akwai irinsu :
•Sangeeta Biljani
•Somy Ali
•Ashwarya Rai
.•Kafrina Muhammad Kaif.
Da sauransu.

Amma a cikinsu Ashwarya Rai ita ce wacce ya ƙarar da soyayyarsa akanta. An haife ta a ranar 1 ga watan Nuwanba 1973. Aishwary Rai ta kasance kyakykyawar jaruma ajin ƙarshe a tarihin fina-finan India sannan ɗaya daga cikin matan da suka lashe kyautar sarauniyyar kyau ta duniya a shekarar 1994.

TARIHIN SOYAYYARSU
Soyayyarsu dai ta fara ne tun loƙacin ɗaukan film ɗin babban mai bada umarnin nan wato ‘Sanjay Leela Bansaley’ wato HUM DIL DE CHUKE SANAM…

Da farko wannan soyayya ta fara gwanin ban sha’awa saboda yadda kowannensu ya ke ƙulafucin ɗan uwansa ta yadda ko ina zasu je duk aikin da za ta je yana wurin haka kuma ita duk wani taro za a gansu a tare.

Haka dai wannan soyayya tayi ta tafiya har na tsawon shekaru biyu.
Kwatsam! A watan Maris na shekarar 2002 wannan soyayya tazo ƙarshe Inda ita Aishwary Rai da kanta ta fara gudun Salman Khan.

Jarumar ta ce ta ɗauki wannan mataki ne saboda jarumin ya fito ya yi iƙrarin cewa bada zuciya ɗaya ya ke zama da ita ba, saidai a na shi ɓangaren ya fito ya ƙaryata hakan a wancan loƙacin.

A wata hira da aka yi da jarumar ta furta cewa soyayya da tayi da shi ba ƙaramin matsala ta kawo a rayuwarta ba,amma ta godewa Allah da abin y azo ƙarshe.

A ya yin da wannan jaruma ke maganar sun rabu da juna, shi kuma a lokacin jarumin ya ke haukan sonta inda ya sha faɗa da mutane da dama akanta musamman idan ya ga kana raɓarta, kamar yayi faɗa da Shah Rukh Khan wanda hakan ya kawo gaba a tsakaninsu wadda aka kai shekaru ana yi amma a yanzu an sasanta.

Jaruma Aishwary ta bayyana cewa Salman Khan a wancan loƙacin da su ke soyayya ya sha dukanta akan yana zarginta tana soyayya da wasu a masana’anta Bollywood, sannan
bayan rabuwarsu ya sha cin mutuncinta da na iyayenta.

A dalilin haka yasa har neman kariya ta kai wurin ƴan sanda,amma shi Salman Khan duk da haka bai daina sonta ba…..

Haƙiƙa jarumi Salman Khan yaso wannan baiwar Allah domin kuwa ya yi abubuwa da dama akanta domin an sha raɗe-raɗin a dalilinta bayan sun samu matsala ya je ya shawu har motarsa ta kwace har ya kashe wani.

A ya yin da ita kuma Aishwarya Rai ta auri jarumi Abishek Amitabh Bachchan a shekarar 2017.

Abin Dana Fahimta
Duk masoyan da suka gama narkewa cikin soyayyar juna, sannan wani saɓani ya shiga tsakaninsu suka rabu, za ka samu akwai maƙaƙin soyayyar juna a zukatan kowanne ɗaya daga cikinsu har abada. Haka Zalika, duk wanda ka so a rayuwa da zuciya ɗaya kuma ku ka rabu, hakan zai iya shafar rayuwarka har abada, wannan gurbin da ka bashi a zuciyarka, ba zaka taɓa baiwa wani ba. Kamar yadda ta faru da Salman Khan da Aishwary Rai.

Daga Mutawakkil Gambo Doko.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button