Kimiya Da Fasaha

Mu Leka Blackhole !(1)

Spread the love

Shin me zaka iya cewa ka sani game da “blackhole”? Bakin rami? To a ina yake?

Masana kimiyya da marubuta da dama tun da jimawa sun kasance masu bincike akan wannan abu da ake kira da blackhole. Tarihi da hujjojin kimiyya sun nuna cewa blackhole ya kasance wani wuri ne (space) a can sararin samaniya mai tsananin karfin maganadiso (gravity) da yake iya janyo duk wani abu komi girmansa ko nauyinsa izuwa cikinsa. Abubuwan da yake iya lakumewa sun hada da taurari, comets, planet, asteroid da sauransu. Wato da zamani ya tafi sai hujjoji suka kara warwarar da lamarin blackhole cewa ba komai bane face wuri (space) mai tsananin karfin gravity sabanin yadda wasu suke tunani cewa rami ne a sararin samaniya.

Yanzu idan akace ka misalta girman tauraro tayaya zaka fara? Bari kaji; rana ta ninka duniyarmu sau sama da 300,000 a nauyi da kuma girma, tauraro daya kuma ya ninka rana sama da sau 100 a girma da kuma nauyi, kenan tauraro daya ya ninka duniyarmu sau miliyoyi a girma. Kuma duk wannan girman nasa haka balckhole yake lakume shi kamar kwayar tsakuwa.

A kimiyyance samuwar duniyarmu ta earth ya faru ne shekaru a kalla 4.3bn da suka shude wanda hakan ya faru ne sakamakon tarwatsuwar wasu taurari da sukayi ruwa da tsaki wajen samar da solar system dinmu wanda ita kanta ranar tamu tauraruwa ce. Irin wannan tarwatsuwar ko fashewar wani abu shi ake cewa cosmic explosion wanda hakan ne makasudin samuwar kaunu gaba dayanta idan muka koma nazariyyar Big Bang wanda ya faru kimanin shekaru 14bn da suka shude. To irin wannan tarwatsewar ne yake zama makasudin samuwar black hole, wanda yake iya kasancewa a gungunan taurari, kamar Milky Way, Andromeda da sauransu. Irin wannan tarwatsewar na samuwar blackhole shi ake kira supernova explosion wato a lokacin da tauraro ya fadada ya fashe haskensa zai ninka na rana sama da sau billion, hakan ne zaiyi sanadiyyar mutuwarsa wanda zai rasa sinadaransa na hydrogen da helium. Sai ya zamana cewa haduwar burbudin wadannan taurari shi yake samar da blackhole kamar yadda masana kimiyya sukace.

Ka dauki misalin haduwar dust (kura) a wuri ko kuma yadda iskar guguwa takeyi; ta hadu da kura da wasu abubuwa tana juyawa da karfi yayinda take game duk abunda ta samu akan hanyarta. Wannan ya faru ne sakamakon karfin janyowa da take da shi. Shi kuwa haduwar dust ka dauka bazai iyayin komai ba sai dai idan ka kai hannu wajensa zai iya hadiyewa. Sannan blackhole kan iya kasancewa a cikin gungun taurari kamar yadda muke da wani blackhole mai suna Sagitarrius A a tsakiyar Milky Way dinmu.

Tauraron da ya mutu shine wanda mansa ya kare wato rayuwarsa tazo karshe, zai koma kamar wani bakin dutse kawai a yayinda zaiyi ta shawagi a sararin samaniya. A wasu lokutan kuma idan supernova explosion ya faru sai ya kai ga iya samar da blackhole. Ka dauki yanayin girman gungun taurari IC 1101 wanda yafi kowane gungu girma shine wanda ya ninka gungun taurarinmu wato Milky Way (inda naje a mafarki… LOL) sau 50 a girma, sannan sama da sau 2,000 a nauyi. Kuma fa akwai taurari sama da trillion a Milky Way dinmu. Wannan fa wai abunda kimiyya ta iya ganowa kenan, to ina abunda bazata iya ba? Lallai tsarki ya tabbata ga Allah!

Sannan duk abunda ya shiga cikin blackhole baya fitowa. Idan kasan yanayin karfin gravity din da yake a bermuda triangle ba sai an fada maka komai ba, kuma wannan a duniyarmu ma kenan. Karfin gravity din da yake a bermuda triangle wanda yake a tsakiyar ruwa shine yake janyo jirage duk girmansu, ya hautsuna su ya janyo su su nutse a cikin tekun. To yanzu idan ka fito daga cikin tekun tayaya zaka fara tashi sama? Karfin gravity din bazai barka ba. To haka blackhole kuma wanda babu wani wuri a sararin samaniya da ya kai shi tsananin karfin gravity. Duk abunda ya shige ciki zai markade ne kamar yadda dalma take narkewa. Sannan akwai wani wuri mafi hatsari a ciki masani sukace shi ake kira da singularity shine yake a tsakiyar blackhole.

Sai mun hadu a kashi na biyu…

✍ Mohiddeen Ahmad
21st May, 2020

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button