Labarai
Mu Sanatoci Zamu bunkasa Siyasar Nageriya ku taimaka Mana da addu’arku ~Inji Malam Shekarau
Sanatan Kano ta tsakiya Malam Ibrahim Shekarau Ya ce Majalisar dattain Nageriya na buƙatar addu’ar ‘yan Nageriya Sanatan ya Rubuta a shafinsa na Facebook Yana Cewa Assalamu Alaikum
Jama’a Barkanmu da Yammacin wannan babbar rana ta Juma’a
INA ROKON
Allah ya karbi ibadunmu
Allah ya kara wa kasarmu albarka
Allah ya bamu zaman lafiya da aminci
Allah ya yi mana muwafika da rahama a lahira
Majalisarmu ta dattijai tana cikin hutun shekara. Duk da haka a tsakanin wannan lokacin, muna zaman kwamitoci da ayyuka na musamman domin bunkasa tsarin siyasar Najeriya da kyautatawa al’umma da suka zabe mu, ta hanyar kafa sabbin dokoki da inganta wadanda ake da su.
Muna bukatar addu’o’inku da karin shawarwari daga gareku, don nasarar wakilci da kuka dora mana.
Nagode