Labarai

Mu ‘yan Arewa muna Cikin hadari Kuma bamu San Ciwon kanmu ba~ Kawu Sumaila

Spread the love

Tsohon Dan Majalisar wakilan Kuma tsohon mataimakin Shugaban Kasa Buhari Kan harkokin Majalisa Hon Kawu sumaila ya rubuta A shafinsa na facebook Yana Mai cewa Abun Dake faruwa a wasu sassa na kasar nan da sunan zanga zangar kin jinin wani sashi na yan sanda babbar manunuyace da ke nuna irin mungun zaman rashin yarda da ke tsakanin yan Nigeria (kudu da arewa) ya sake nuna mana mu yan arewa chewar muna chikin hatsari sabo da kawaichi ko rashin sanin chiwon kanmu da kin junanmu da rashin Kula da matsalolin mu,ina ga akwai bukatar chikin gaggawa mu masu magana da harshen HAUSA muyi karatun ta nutsu mu Duba Halin da muke chiki a SIYASA,TaTTALIN ARZIKi DA TSARIN ZAMAN TAKEWAR MU mu duba halin da muke chiki yau kuma ina Muka dosa,

Ya Zame mana dole a samu wasu a chikin mu su samar da zama na musamman (conference) a yi nazari a tattauna don Samun mafuta,kuma a bawa kowa dama ya Bada gudunmowarsa ta hanyar baiwar da Allah ya bashi kuma wannan tattaunawa Ayi ta da Harshen Hausa don bawa kowa dama, Lokachi yana Neman Kure mana barna tana sake samun gindin zama a tsakanin nin mu wahalhalu da matsi hade da Kunchin rayuwa suna sake mamaye mu,ko dai chikin gaggawa mu Fara shiri na tunkarar matsalolin mu ko kuma abun da muke gudu ya samemu ba shiri,

Allah ya kiyaye.Na sani da yawa za suga chewa tatsuniya nake don suna ga suna amfana da halin da ake chiki to su sani ba mai tsara in fitana ta baiyana. A kula sosai nache Hausa ne don shine ce yaren da mafi yawan yan Arewa suke amfani da shine a mu’amila ta yau da gobe kuma mune muke fama da Manyan fitunu (Taaddanchi,Satar mutante, Rigimar addini da Talauchi.)Allah ya sa mu dache.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button